Shari'ar Oscar Pistorius ta dauki sabon salo

Pistorius
Image caption Pistorius

Rundunar 'yan sandan Afrika Ta Kudu ta ce za a nada sabon jagoran masu gabatar da kara kan shari'ar kisan kai da ake yi wa Oscar Pistorius, zakaran tsren nakasassu a Afrika ta Kudu.

An ambaci wani kwamishinan 'yan sanda yana cewa zasu tara wasu kwararru kuma gogaggun jami'an gudanar da bincike.

Hakan na zuwa ne bayan da ta tabbata cewa, dansandan da ke bincike a shari'ar shi ma yana fuskantar tuhumar kisan kai da ta auku kamar shekaru biyu baya.

Shi dai dan tseren, Oscar Pistorius, ana zarginsa ne da kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp.

Sai dai wata mai magana da yawun hukumar gabatar da kara ta kasar, Bulewe Makeke, ta ce zargin ba zai shafa wa shari'ar da ake wa Oscar Pistorius, kashin kaji ba.

A gobe Juma'a, ake sa ran za a yanke hukunci game da shari'ar neman belin da aka shigar kan Mr Pistorius.

Karin bayani