Hugo Chavez yana fama da matsalar numfashi

Image caption Hugo Chavez

Gwamnatin Venezuela ta ce har yanzu shugabanta mara lafiya, Hugo Chavez, yana fama da matsalar numfashi, fiye da watanni biyu bayan da aka yi masa tiyatar cutar sankara a karo na hudu.

Ministan Sadarwa,Ernesto Villegas, ya ce ana kula da Mista Chavez a wani asibitin sojoji da ke Caracas inda aka kai shi tun bayan dawowarsa daga Cuba a farkon wannan makon.

An ce shugaban Venezuela na fama da matsalar numfashi tun bayan da aka masa tiyatar karshe.

Ministan sadarwar ya ce:" har yanzu matsalar numfashin da shugaban ke fama da ita, wacce ta sanya aka yi masa aiki, tana nan; amma ana kokarin shawo kanta. Tuni likitoci suka fara kokarin magance matsalar''.

Karin bayani