Morsi yana so a gudanar da zabe a Masar

Image caption Mohammed Morsi

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, ya yi kira da a fara gudanar da zaben majalisun dokoki daga karshen watan Aprilu mai zuwa.

Wata sanarwa da shugaban kasar ya fitar ta ce za a fara zaben ne daga ranar 27 ga watan Aprilu, a kammala a karshen watan Yuni.

Sanarwar ta ce za a gudanar da zabukan ne a matakai gudu hudu, kuma daga yanki zuwa yanki.

Za a gudanar da zaben ne daki-daki a yankuna daban-daban ne saboda karancin masu sanya idanu a kan zabe.

Karin bayani