'Yan adawar Syria za su zabi Fira Minista

Jagoran 'yan adawar Syria Moaz Al Khatib
Image caption Ana ci gaba da rikici a Syria

Babbar kungiyar yan adawa a Siriya ta ce za ta gudanar da taro a mako mai zuwa domin zabar Firaminista wanda zai jagoranci gwamnatin wucin gadi da za ta rika gudanar da ayyukanta daga yankunan da yan tawayen suka karbe a Siriya.

Bayan taro na kwanaki biyu da suka yi a birnin Alkahira, hadaddiyar kungiyar yan adawar wadda ake yiwa lakabi da "Syrian National Coalition" a turance ta ce taron shirin kafa gwamnatin wucin gadin za'a yi shine a birnin Santanbul na kasar Turkiya a ranar biyu ga watan Maris.

A cikin Siriya, yan gwagwarmaya sun ce an kaiwa birnin Aleppo harin rokoki inda aka kashe a kalla mutane goma sha biyu aka kuma ragargaza gidaje da dama.

Karin bayani