Amurka ta sake tura sojoji 40 zuwa Nijar

Mahamadou Isoufu-Shugaban Nijar
Image caption Barack Obama ya kara tura sojoji zuwa Nijar

Shugaban Amurka, Barrack Obama ya kara tura wasu sojojin Amurka 40 zuwa Jamhuriyar Niger, domin taimakawa wajen tattara bayanan sirri

Hakan na faruwa a daidai lokacin da sojojin Faransa tare da hadin guiwar sojojin wasu kasashen Africa ke ci gaba da fafatawa da kungiyoyin 'yan tawaye masu kishin islama a kasar Mali.

Fadar White House ce dai ta bayyana haka, a wata wasika data turawa majalissar dokokin Amurkar.

Sojojin Amurkar zasu bi sahun takwarorinsu 60 ne wadanda dama can Amurka ta tura zuwa Jamhuriyar ta Niger.

Kamar yadda wasikar ta bayyana, an tura sojojin ne ranar larabar da ta wuce.

Dama a can baya, wani jami'in Amurka ya ce ma'aiakatar tsaron Amurkar na shirin girke jiragen da basa amfani da direbobi, mai yiuwa a Jamhuriyar Niger, domin taimakawa wajen tattara bayanai akan kungiyar Al-Qaeda a yankin Maghreb da kuma abokan kawancenta a yankin.

Karin bayani