Gwamnatin Amurka ta kai karar Armstrong

Image caption Lance Armstrong

Gwamnatin Amurka ta kai karar shahararren dan tseren keken nan, Lance Armstrong, tana zarginsa da yi wa hukumar aikewa da wasiku ta kasar zamba-cikin-aminci.

A watan jiya ne dai Mista Armstrong, wanda sau bakwai yana lashe gasar tseren kekuna ta Tour de France, ya amince cewa ya yi amfani da kwayoyin kara kuzari.

Hukumar aikewa da wasikun Amurka tana so ne Armstrong ya biya ta kudin da ta kashe a kansa, domin kuwa ma'aikatar shari'ar kasar ta ce a yarjejeniyar da aka kulla da shi, ya amince cewa ba zai yi amfani da kwayoyin kara kuzari ba.

Sai dai lauyan Armstrong ya ce suna tattaunawa da hukumar don ganin bai biya wadannan kudade ba.

Karin bayani