Amurka ta dakatar da jirgin F-35

Image caption Jirgi samfurin F35

Rundunar sojin Amurka ta dakatar da dukkanin jiragenta na yaki samfurin F-35 su fiye da hamsin daga tashi, bayan wani bincike da ta yi ya nuna cewa injin daya daga cikin jiragen ya tsage.

Wannan shi ne karo na biyu a kasa da watanni biyu da Amurka ke dakatar da jiragenta daga tashi saboda matsalar na'ura.

Jirgin samfurin F35 na daga cikin jiragen Amurka na yaki da ake takama da su.

An sayar da irin wadannan jirage ga wadansu rundunonin sojin kasashen duniya, ciki har da rundunar sojin Burtaniya.

Jirgin F-35 shi ne jirgin yaki mafi tsada da Amurka ta samar, inda aka kashe kusan dala biliyan 400 wajen kera jirage 2400.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ya yi wuri a yi hasashen irin tasirin da wannan matsala za ta haifar.

Karin bayani