Masu zabe na kada kuri'a a Italiya

Fastocin 'yan takara a Italiya
Image caption Jam'iyyun siyasar Italiya na gwagwarmayar darewa kan karagar mulki

An bude rumfunan zabe a Italiya, a daya daga cikin manyan zabukan da aka sanyawa ido sosai a cikin shekaru masu yawa.

Ana gudanar da zaben ne yayin da ake fama da koma-bayan tattalin arziki da kuma matakan tsuke bakin aljihu wadanda gwamnatin kwararru da Mario Monti ya jagoranta ta kaddamar.

Wannan ne karo na farko da za a gudanar da zabe tun bayan da aka tsige Firayim Minista Silvio Berlusconi daga mukaminsa a shekarar 2011.

Wa'adin mulkin gwamnatin kwararrun dai ya zo karshe, kuma jam'iyyun siyasar kasar na sake fafatawa a yunkurinsu na darewa karagar mulki.

Mista Berlusconi dai ya yi ta sadaukar da komai a yunkurinsa na komawa kan kujerar day a bari.

Ya yi alkawarin kubutar da Italiyawa daga matakan tsuke bakin aljihun da gwamnati mai barin gado ta kakaba musu.

Ya kuma yiwa babban abokin hamayyarsa Pier Luigi Bersani na jam'iyyar Democratic Party ta masu matsakaicin ra’ayin mazan jiya ba-zata.

Mista Bersani dai na batu ne na kawo sauye-sauyen da za su fitar da kasar daga matsalar da take fuskanta, kuma mai yiwuwa jam'iyyarsa ta kara karfi a wannan zabe.

Sai dai kuma a lokaci guda wata kungiya ta talakawa mai suna Five Star Movement wadda ke adawa da tsarin shugabancin kasar ta yi tasiri a yakin neman zabenta.

Don haka ba zai yiwu na a irin wannan yanayi a iya hasashen wanda zai jagoranci kasar ta Italiya bayan an kammala kidaya kuri'u.

Karin bayani