Amurka ta tura sojoji Nijar

Amurka ta aike dakarun soja dari zuwa jamhuriyar Niger domin hada gwiwa da sojojin kasar Faransa dangane da yakin da suke yi da yan ta'adda a kasashen yankin Sahel.

A jiya ne shugaban Amurka, Barack Obama ya tabbatar da aike dakarun zuwa Niger.

Sai dai gwamnatin Niger din ba ta ce uffan ba dangane da wannan lamari.

A watan da ya gabata ne dai kasashen na Nigerr da Amurka suka sa hannu a kan wata yarjejeniyar tsaro da wasu 'yan kasar ta nijar ke ganin wata alama ce ta ci gaba da yiwa Niger din mulkin mallaka.

Sojojin na Amurka dai sun je Nijar din ne da makamansu, wanda shugaba Obama ya ce za su rike ne domin kare kansu.

Tura sojojin Amurkan Nijar dai yawo kasa da wata guda bayan da Amurka ta girke jiragenta marasa matuka a kasar, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan 'yan kasar ta Nijar.