Baraka tsakanin 'yan adawar Syria

'Yan adawar Syria
Image caption 'Yan adawar Syria

Kungiyar 'yan adawar Syria ta National Coalition ta bada sanarwar cewa ta yanke shawarar kin halartar wani taron kasashe aminan Syria da za'a yi a Roma watan gobe, koma ta amsa goran gayyatar tattaunawa a Mascow da Washington.

Kungiyar hadakar 'yan adawar ta Syria ta ce ta yanke wannan shawara ne domin nuna rashin jin dadinta ga abin ta ta kira gazawar kasashan waje wajan dakatar da rikicin na Syria, ta kuma dora alhakin tura makamai zuwa Damascus akan kasar Rasha.

Babban muhimmin abun da wannan shawara ta kauracewa tarukan diplomasiyya na kasa da kasa akan syria zata haifar shi ne na yin kafar angulu ga shirin da shugaban kungiyar hadakar 'yan adawar, Moaz al-Khatib ya kaddamar.

Makwanni 3n da suka wuce ya bada wata sanarwar bazata ta cewa a shirye ya ke ya gana da wakilan gwamnatin Syrian domin tattaunawa kan yadda za'a kawo karshen zibda jinin da ake a kasar.

Kuma gwamnatocin kashen waje sun yi matukar marhabin da wannan mataki ciki har da Rashawa, inda kuma aka gayyace shi zuwa Moscow da Washington.

To yanzu wadannan ziyarce-ziyarce baza su samu ba.

Jami'an diplomasiyyar dake neman hanyar siyasar da za'a warware rikicin ba su ji da din wannan mataki ba.

Sai dai a fili ta ke cewa shugabannin 'yan adawar na fargabar cewa martabarta zata zube kuma za su iya kaucewa ainahin abin da ke wakana a kasa idan har ta bi wata hanyar da ta hada da mika wuya ga gwamnatin da bata nuna alamar sauka ba.

Har ila yau basa jin dadin yadda gwamnatin ke ci gaba da kai hare hare a wuraran dake hannun 'yan tawaye a Aleppo da makamai masu linzamin da kasar Rasha ke sama mata, inda ake ritsawa da mutane da dama.

Akwai zargin cewa kwararrun kasar Rashan ne ke harba su dan haka basa daukar Rashan a matsayin kasar da zata iya shiga tsakanin.

Karin bayani