Afghanistan na nuna yatsa ga dakarun Amurka

Dakarun Amurka a Afghanistan
Image caption Dakarun Amurka a Afghanistan

An baiwa dakarun Amurka na musamman wa'adin nan da makonni biyu su fice daga yankin Wardak mai matukar muhimmanci a Afghanistan.

Wani kakakin shugaban Afghanistan, Hamid Karzai yace, an dauki wannan mataki ne bayan zargin cewa, dakarun Afghanistan din dake aiki da takwarorinsu na Amurka suna da hannu a salwantar jama'a da kuma azabtarwa.

Kakakin shugaba Hamid Karzai, Aimal Faizi yayi karin haske akan wannan mataki, inda ya ce ayyukan sojan da dakarun Amurka na musamman ke yi a wannan lardi, ana yinsu ne tare da hadin gwiwar dakarun Afghanistan.

Lardin Wardak dai yana tsakiyar Afghanistan ne kuma an maida hankali akan yankin wajen yaki da masu tada kayar baya saboda ta yankin ne 'yan Taliban suke samun damar kai hare-hare a babban birnin kasar Kabul.

Karin bayani