Zaban Paparoma na fuskantar matsala

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma Benedict

Dubban mutane ne sukai dafifi a dandalin St Peter a birnin Roma domin samun addu'o'in paparoma na ranar lahadinsa ta karshe a kan shugabancin cocin.

Ranar alhamis mai zuwa ce zai sauka daga mukamin paparoma bayan shafe shekaru takwas a shugaban cocin.

Paparoma Benedict ya gudanar da aikinsa na ranar lahadi ta karshe a matsayin bishop na Roma, inda ya leko ta tagar dakin karatunsa dake kallon dandalin St Peter, domin yiwa dubban masu ziyarar ibada da 'yan awon bude ido addu'o'i.

Sai dai kuma rikicin da ya kunno kai a cocin wanda ya hada da Cardila na yankin Scotland da na Amurka ya kankane kokarin da ake na nada sabon paparoma na zai gane shi.

Wasu mabiya darikar Katolikan na kira ga Cradinal O'Brien daga yankin Scotland da kuma Cardinal Mahony daga Los Angeles da su kauracewa zaban paparoman da za'a yi watan gobe.

Tuni wasu mabiya cocin Katolikan suka mika takaddar kokensu dauke da sahannun dubban mabiya darikar suna neman cardilan Mahony na da kada ya shiga sahun wadanda za su zabi sabon paparoman.

Chris Pompelly shi ne daraktan sadarwa da cigaba na kungiyar hadin kan mabiya darikar Katolika wato Catholic United, kuma shi ne ya gabatar da takaddar koken nasu:

Sai dai kuma Fadar Vatican ta yi allawadai cikin fushi da duk wani yunkuri na sa sharadi kan 'yancin cardinal cardila din da za su zabi paparoman da suke san ya shugabanci cocin nan gaba.

A ranar laraba ne dai Paparoma Benedict zai yi fitarsa ta karshe a baina jama'a a matsayinsa na shugaban cocin.

Karin bayani