An sami sabani tsakanin 'yan tawayen M23

Kungiyar 'yan tawaye ta M23
Image caption 'yan tawayen M23 sun kafsa fada da juna

'Yan sa'oi kalilan bayan shugabannin kasashen Afrika sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya da za ta taimaka wajen kawo zaman lafiya a jamhuriyar demokradiyyar kongo, wasu bangarori biyu da ba sa ga maciji da juna a kungiyar 'yan tawaye na M23 sun kafsa fada da junan su.

Fadan ya auku ne a yankin arewa maso gabashin yankin Rutshuru, inda mutane takwas su ka rasa rayukansu.

Fadan ya barke ne tsakanin magoya bayan kwamandan sojojin M23 Janaral Sultani Makenga da kuma jagoran siyasar kungiyar Jean Marie Runiga.

Masu aiko da rahotanni sun ce an samu sabani tsakanin bangarorin biyu ne kan yadda za a tunkari yarjejeniyar samar da zaman lafiya a yankin .

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban ki Moon, ya yi gargadin cewa, yarjejeniyar masomi ne kawai, na kawo zaman lafiya a jamhuriyar demokradiyar Kongo.

Karin bayani