An saka hoton bidiyon Faransawan da aka kama a intanet

Faransawan da aka sace
Image caption Iyalin da aka sace sun bayyana a hoton bidiyon da aka saka a Youtune.

Wani hotan bidiyo da aka sa a shafin You Tube na Intanet ya nuna Faransawan nan bakwai da wasu 'yan bindiga suka sace a Kamaru.

Kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus sunna liddaa'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram ce ta yi ikirarin fitar da wannan bidiyon, tana mai cewa Faransawan bakwai su na hannun ta.

A cikin bidiyon dai Kungiyar ta yi barazanar za ta kashe Faransawan matukar ba a biya masu wasu bukatunsu ba, wadanda suka hadar da sako wasu 'yan kungiyar da ake rike da su a gidajen kaso.

Hoton bidiyon dai ya nuna wasu mutane uku fuskokinsu a rufe dauke da bindigogi sanye da kaki irin na sojoji tare da Faransawan.

Biyu daga cikin mutanen da suka boye fuskokinsu na tsaye, daya kuma a zaune wanda shi ne yake karanta jawabin dake cikin sakon bidiyon a harshen larabci.

A saki Fursunoni

Daga bayan wadannan mutane kuwa akwai bakin kyalle dauke da kalmar Lailaha ilallahu, da kuma zanen bindiga a kowane gefe na bakin kyallen.

Wanda ke karanta jawabin dai ya yi ikirarin cewar su 'ya'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram, kuma su ke rike da wadannan Tuwaran kasar Faransan, ya kuma bukaci a sako masu fursononinsu da ake rike da su a Kasashen Najeriya da kuma Kamaru.

A cikin bidiyon dai mutumin ya gargadi Kasar Faransa da cewa tana yaki ne da addinin musulunci a Mali, kuma ya yi gargadin cewar idan har ba a sako 'ya'yan kungiyar da ake rike da su din ba, to kuwa zasu kashe wadannan Turawan.

Turawan dai a cikin bidiyon, sun nuna cewa suna cikin koshin lafiya, babu kuma wata alamar tagayyara tare dasu.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransan dai a wata sanarwar da ta fito daga ministan harkokin wajen Faransan ta bayyana matukar kaduwarta game da hoton bidiyon, tana mai cewa hotunan na nuna tsagwaran rashin imani.

A makon da ya gabata ne dai wasu mutane suka sace iyalin Faransawan.

Tun da farko dai shugaban Faransan ya yi zargin cewar kungiyar Boko Haram a Najeriya ita ta sace 'yan kasar tasa.

Gwamnatin Faransan ta kuma yi imanin cewar an yi awon gaba da su ne zuwa cikin Najeriya

An yi dai ta samun rahotanni masu karo da juna tun daga wancan lokaci game da makomar mutanen da kuma yunkurin da ake na ceto su.

Karin bayani