Matsalar zaben kananan hukumomi a Nageria

'yan Nigeria na kada kuri'a
Image caption 'yan Nigeria na kada kur'a a rufunan zabe

A Nijeriya, wata babbar matsala da masana ke cewa na barazana ga dimokuradiyyar kasar ita ce ta rashin takamaiman tsarin gudanar da zabukan kananan hukumomi, inda kowace jiha kan gudanar da zabukanta a duk lokacin da ta bushi iska.

Hakazalika, duk jam'iyya mai mulki a matakin jiha, ita ce kan lashe dukkan kujerun kansiloli da na shuwagabannin kananan hukumomi idan aka yi zabukan, yayin da jam'iyyun adawa kan tashi a tutar babu kome karfinsu a jihar kuwa.

Jihar da hakan ta faru a baya-bayan nan ita ce jihar Gombe, inda hukumar zaben jihar wato GOSIEC ta ce jam'iyyar PDP mai mulki ce ta lashe ilahirin kujerun shugabannin kananan hukumomi da kuma kansiloli a zabukan da aka gudanar a kananan hukumomi goma sha daya na jihar, sakamakon da 'yan adawar jihar suka yi watsi da shi su na masu cewar a ganin su ba a ma yi zabe ba.

Sai dai shugaban jam'iyyar adawa ta CPC a jihar Gombe Barista Abdu Baba ya ce saboda irin cin mutunci da musgunawa da gwamnatin PDP ta musu a zabukan, da ma yadda ake gani a jihohi da dama a Najeriya, ya wajaba a karbe ragamar gudanar da zabukan kananan hukumomi daga hannun gwamnatocin jihohi.

Sai dai magoya bayan gwamnatin jihar sun ce an gudanar da zabukan yadda ya kamata, don haka babu dalilin karbe su daga hannun jiha.