Cardinal O'Brean ya yi murabus

Image caption Cardinal O'Brean; wanda yayi murabus

Jagoran ɗarikar Roman Katolika a Burtaniya ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon zargin da ake masa cewar bai ɗauki matakan da suka dace ba kan wasu malaman cocin shekaru talatin da suka wuce.

Cardinal Keith O'Brien, ya ce Paparoma Benedict ya amince cewa murabus din na sa, daga shugabancin cocin Scotland, zai fara aiki nan take.

Mai magana da yawun fadar Vertican ya ce aikinmu ne mu amince da murabus din da yayi ta bangaren Paparoma, kamar yadda tsarin mulki na Canon Law ya tanada.

Cardinal O'Brien, ya ƙara da cewa ba zai shiga cikin ƙuri'ar da za a kaɗa domin zaɓen sabon Paparoma ba duk da cewa yana da ikon yin hakan, saboda har yanzu shi Cardinal ne.

Wakilin BBC kan harkokin addini ya ce wannan zai ƙara matsin lamba ga sauran Cradinals waɗanda ake zargi da nuna gazawa kan yadda suka tunkari batun lalata da ƙananan yara.