An soma samun sakamakon zaben Italiya

Zabe a Italiya
Image caption An soma samun sakamakon zabe

Sakamakon farko-farko na zaben kasar Italiya ya nuna cewa babu wadanda su ka samu rinjaye a zaben da aka kada.

An ce jam'iyyar democractic Party karkashin jagorancin Pier Luigi Bersani ce kan gaba a majalisar dokokin kasar, sai dai kuma wani kawance karkashin jagorancin tsohon Pira minista Silvio Berlusconi na da alamar samun nasara a majalisar dattijai.

Masu sharhi na ganin cewa idan wannan sakamakon ya tabbata, to gwamnati ta gaba da za a kafa, ba za ta samu karfin aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo bunkasar tattalin arziki ba.

Masu zabe dai sun yaba da rawar da jam'iyyar shararren dan barkwancin nan Beppe Grillo ta taka.

Karin bayani