Al-Qa'ida ta gargadi 'yan tawayen Mali

Abdel Malek Droukdel
Image caption Abdel Malek Droukdel ya nuna damuwa kan yadda aka yi saurin kafa shari'ar Musulunci a Mali

Wasu takardu da 'yan tawayen Mali suka bari lokacin da suka fice daga arewacin kasar, sun nuna mai yiwuwa sabani a tsakaninsu ne ya kaisu ga rashin nasara a fagen daga.

A wata wasika da wani shugaban kungiyar Al-Qa'ida ya aikewa kwamandan 'yan tawayen na kungiyar Ansaruddin a Mali, ya soke su dangane da tursasa shari'ar Musulunci cikin hanzari.

Shugaban Kungiyar Al-Qaida a yankin Magrib da ke Aljeriya, Abdel Malek Droukdel, ya yi hasashen yiwuwar Faransa za ta kai farmakin soji a Malin.

Wasu 'yan jarida ne suka gano takardun a garin Timbuktu na arewacin kasar ta Mali.

Kuma wata Jaridar Faransa mai suna Liberation ta wallafa wasikar mai shafuka 79.

A cewarsa shirin kafa shari'ar Musulunci a Mali "jariri ne wanda ke kwanakinsa na farko na haihuwa".

Yadda aka rubuta wasikar na kama da yadda shugaban kamfani ko hukuma ke bayar da umarni ga matsakaitan jami'ansa.

Haka kuma jagoran na Al-Qaida ya ce ta hanyar lalata dadaddun hobbarai da hana mata fita daga gidajensu da kuma hana yara wasa, masu fafutukar Islaman sun rasa goyon bayan jama'ar yankin.

Wadannan abubuwa ne kuma suka ja hankalin kasashen duniya ga kasar ta Mali da abinda ke faruwa.

Karin bayani