Sabuwar tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran

Shirin nukiliyar Iran
Image caption Shirin nukiliyar Iran

An bude taron tattaunawa ta kasa da kasa, kan shirin nukiliyar Iran a birnin Kazakhstan, inda manyan kasashen duniya shida ke halarta.

Kasashen sun hada da Amurka da Rasha da China da Jamus da Birtaniya da kuma Faransa.

Tattaunawar ita ce irinta ta farko a cikin watanni shida da suka gabata.

Kasashen dai na son Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya, su kuma su sassauta mata takunkumin da suka kakaba mata.

Amurka da Rasha sun yi gargadin cewa lokaci na kurewa na warware jayyaya game da shirin na Iran.

Kasashen na zargin Iran na kera makaman nukiliya ne, amma ita kuma ta musanta hakan, tana mai cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne.