Kiki-kakar siyasar Italiya ta girgiza kasuwannin kudi

Silvio Berlusconi da Pier Luigi Bersani
Image caption An shiga rashin tabbas a Italiya

Kiki-kakar siyasar da ta biyo bayan kasa samun tabbataccen sakamakon babban zaben da aka yi a Italiya ta girgiza kasuwannin kudi.

Darajar Kasuwannin hannayen jari a Italiya da na sauran kasashen duniya ta ragu, kamar kuma yadda ta shafi kudin Euro yayinda kuma kudaden ruwan bashin da Italiyar ta ci suka karu.

Wannan duka na faruwa ne lokacin da 'yan kasuwa da 'yan siyasa ke nazartar gazawar da kawancen masu matsakaicin ra'ayin sauyi na Pier Luigi Bersani ya yi na samun rinjaye a dukkanin majalisun dokokin kasar.

Tsohon Fira Minista Silvio Berlusconi ya ce dukkanin jama'iyyun siyasar za su bukaci yin sadaukarwa domin kafa wata gwamnati

Sai dai wani wakilin BBC a Birnin Roma ya ce akwai yiwuwar yin wani zaben karo na biyu a cikin watanni, idan dai ba Beppe Grillo da ya bayar da mamaki a zaben ya yanke shawarar shiga cikin wani kawance ba.

Karin bayani