Zaben Italiya ya haifar da rashin tabbas

Ma'aikatan zabe na bude akwatunan zabe a Italiya
Image caption Ma'aikatan zabe na bude akwatunan zabe a Italiya

Italiya na fuskantar kiki-kakar siyasa bayan zaben da ya samar da majalisar dokokin da babu jam'iyya mai rinjaye a cikinta.

Ga alama tsarin zabe mai sarkiya da kuma tsananin rashin gamsuwa da harkar siyasa a kasar ta Italiya ne suka hadu suka haifar da barazanar aukuwar kiki-kakar.

Hakazalika, zaben—wanda ga alama tasirinsa ba zai taka kara ya karya ba wajen warware matsalolin da kasar ke fuskanta—ka iya haifar da wani mummunan yanayi na rikita-rikitar siyasa.

Ko da yake ba a fitar da sakamakon karshe na zaben ba, kawancen jam’iyyu masu matsakaicin ra’ayin kawo sauyi a karkashin jagorancin Pier Luigi Bersani na da mafi karancin rinjaye a majalisar wakilai, amma jam'iyyu masu matsakaicin ra’ayin mazan jiya, wadanda tsohon Firayim Minista Silvio Berlusconi ke yiwa jagoranci, sun nace cewa kai-da-kai aka yi.

Ga shi kuma babu wanda ya samu gagarumin rinjayen da ake bukata a majalisar dattijai, al’amarin da ka iya tilasta gudanar da wani zaben nan da watanni kadan.

Sakataren jam’iyyar Il Popolo della Liberta ta Mista Berlusconi, Angelino Alfano ya ce ya ji dadin sakamkon zaben:

“Wannan sakamako ne mai kyau, kai ina ma ganin sakamako ne mai ban mamaki.

“Mun yi matukar farin ciki kuma mun gamsu sosai—tuni na yi magana da Mista Berlusconi na yi masa godiya a madadin jam’iyyarmu saboda jajircewarsa ce ta haifar da wannan sakamako”.

Shi kuwa sakataren jam’iyyar Democratic Party ta Mista Bersani, Enrico Letta, cewa ya yi siyasar Italiya na fuskantar fadawa cikin rudani.

A cewarsa, “Kimar siyasar Italiya ta zube saboda abin kunyar da ’yan siyasa ke tafkawa, kuma saboda wahalhalun da jama’a ke fama da su a ’yan shekarun nan.

“Wajibi ne a farfado da kimar siyasa ta hanyar amsa wadansu muhimman tambayoyi saboda amsoshin da muka gani a yau ba su wadatar ba”.

Wani abin da ya bayar da mamaki a zaben dai shi ne yadda goyon bayan da kungiyar Five Star Movement ke samu ya bunkasa sosai.

Kungiyar dai ta wadansu talakawa ne masu adawa da hukumomi a karkashin jagorancin wani mai wasan barwanci, Beppe Grillo.

Shi kuwa Mario Monti, wanda ya jagoranci kawo sauye-sauyen tattalin arziki, a matsayi na hudu ya kare.

Tuni dai rashin tabbas din da sakamakon zaben ya haifar ya sa hantar kasuwannin hannayen jari ta kada.

Italiya ce dai kasa ta uku mafi karfin tattalin arziki a Turai kuma masu zuba jari na fargabar cewa idan sakamakon zaben ya kai ga rudanin siyasa to hannun agogon nasarar da aka samu a yunkurin magance matsalar tattalin arzikin kasashe masu amfani da kudin euro zai koma baya.

Karin bayani