Ba mu da matsala da shugaban kasa —Nyako

Gwamna Murtala Nyako
Image caption Gwamna Murtala Nyako: 'Mu dai masu hankali ne...'

A Najeriya wani zaman da Kungiyar Gwamnonin Jihohi ta yi da niyyar zaben sabon shugaba ya tashi ba tare da an yi zaben ba, sakamakon zargin da ake yi cewa bangaren shugaban kasar ne ke neman hanyar karya-lagon kungiyar.

Kungiyar Gwamnonin dai ta dage zaman nata ba tare da ba da wani kwakkwaran dalili ba.

Sai dai Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa ya shaidawa BBC cewa, “Ba mu yi zabe ba domin ba zabe ba ne magana [mai muhimmanci a] yanzu; mu yi shiri tukunna—in mun shirya wannan abin, za mu san wanene cikinmu ya cancanta ya shugabanci wannan [kungiya]”.

Dangane da batun yunkurin fadar shugaban kasa na karya lagon gwamnonin kuwa, Gwamna Nyako cewa ya yi:

“Mu dai [dukkanmu] masu hankali ne. duk wata magana da aka fada mana idan ba mu gamsu ba, abin bai mana dadi ba, za mu hau ne a garaje?”

Rahotanni dai na nuna cewa gwamnoni da dama ba su ji dadin wani mataki da jam’iyyar PDP ta dauka ba, na nada sabon shugaban kungiyar gwamnoni ’ya’yan jam’iyyar, wato Gwamna Godswill Akpabio na Akwa Ibom, gabannin karewar wa’adin shugaban kungiyar gwamnoni ta kasar wato Rotimi Amaechi.

Karin bayani