Radadin satar 'yan kasashen waje a Najeriya

Rundunar 'yan sanda Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike
Image caption 'Yan sandan Najeriya sun ce suna ci gaba da bincike kan satar 'yan kasashen waje a Jama'are

Jama’ar yankin Jama’are dake jihar Bauchi a Najeriya sun bayyana cewa suna jin radadi matuka a harkokin rayuwarsu na yau da kullum da kuma tattalin arziki sakamakon awon gaba da wadansu ma’aikata ’yan kasashen waje na kamfani mafi girma a yankin wato SETRACO.

Kimanin makwanni biyu ke nan dai tun bayan da ’yan bindiga suka sace mutanen bakwai daga gidan kwanan ma’aikata na kamfanin mai aikin gine-gine—musamman na hanyoyin mota—a Najeriya, kuma kawo yanzu babu duriyarsu.

Bayan fruwar lamarin ne dai hukumomin kamfanin suka rufe ayyukansu a yankin na Jama’are sannan suka kwashe ma’aikatansu daga yankin saboda tsaron lafiyarsu.

Sai dai kuma tasirin hakan ta fuskar tattalin arziki shi ne harkoki sun durkushe, daruruwan ’yan Najeriya sun rasa ayyukan yi.

Shugaban Majalisar Matasan Jama’are, Malam Hassan Usman, ya shaida BBC cewa al’ummar yankin sun shiga tsaka mai wuya.

“Wannan al’amari ya daga mana hankali, ya ja mana ci baya fiye da kima…matasanmu fiye da dari hudu suna aiki a wannan kamfani; akwai kuma mutane kimanin dari uku ’yan wasu jihohi daban-daban [wadanda] zamansu ya kawo ci gaba tattalin arziki gare mu saboda za su kama haya, za su yi sayayya—kusan rabin albashinsu a wajenmu suke kashe shi.

“Amma sakamakon rufe wannan kamfani zaman banza zai karu, talauci zai karu, da kuma rashin aikin yi”.

Yayin da jama’a ke fargaba da kokawa kan illolin da matakin rufe kamfanin ya jawo ga tattalin ariki, shi kuwa jami’in hulda da jama’a na kamfanin na SETRACO a Najeriya, Mista Abu Malik, a wata hira da ya yi da wakilin BBC Is’haq Khalid, ya ce sun rufe kamfanin ne na wucin gadi ba na dindin-din ba a yankin na Jama’are.

’Yan kasashen wajen da aka kama ma’aikatan kamfanin na SETRACO sun hada da ’yan Lebanon biyu, da ’yan Syria biyu, da dan Burtaniya da dan Italiya da kuma dan Girka.

Idan za a iya tunawa wata kungiya mai suna Jama’atu Ansarul Musulmina fi Biladil Sudan ta yi ikararin kama su saboda abin da ta kira zaluncin kasashen Yamma ga musulmi kamar a Mali da Afghanistan.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi, Hassan Muhammad Auyo, ya bayyana cewa har yanzu ana nan ana bincike a kokarin da jami’an tsaro ke yin a kubutar da mutanen.

Karin bayani