Kasafin kudin Najeriya na shekara ta 2013

A Najeriya, dazu ne shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya sanya hannu a kan kasafin kudin kasar na shekarar 2013 watau Naira tiriliyan 4.986 kan gangar mai, dala 79.

Kazalika shugaban ya sanya hannun ne duk kuwa da cewa ba a warewa hukumar da ke kula da kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasar, SEC ko sisi a kasafin kudin b,a sakamakon takaddamar da ke tsakanin hukumar da 'yan majalisar.

A baya dai batun sanya hannu a kan kasafin kudin ya jawo rashin jituwa tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar da shugaban kasar game da tsayar da farashin da za a sayar da gangar man, inda bangaren shugaban kasar ya dage cewa za a sayar da gangar man ne a kan dala 75.