Nijar ta ce akwai dakarun Amurka da na Faransa a kasarta

Jirgin yaki maras matuki
Image caption Jirgin yaki maras matuki

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun amsa cewa lallai akwai sojojin Amurka da na Faransa a kasar.

Bayanin hakan ya fito ne yayinda kakakin gwamnatin Nijar, Malam Marou Amadou ke amsa cewar hukumomin kasar sun kyale Amurka da Faransa su girke wasu jiragen yaki marasa matuka da zasu rika sintiri a yankin, domin kara karfafa tsaro.

Ya ce kasancewar Nijar ba ta da karfin aiwatar da wannan aiki ya sa ta kyale jiragen, domin zasu taimaka wajen tabbatar da daukar matakan da suka dace a kasar Mali makwabciyarta, mai fama da rikici, wajen samun bayanan sirri.

Nijar din ta kuma musanta rahotanin dake cewa an raunata wasu sojojin kasarta shidda dake aikin kiyaye zaman lafiya a Mali.

Karin bayani