Sarkin Kano ya koma gida

Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero
Image caption Sarkin Kano ya koma gida daga London

Rahotannin daga Kano a arewacin Nigeria na cewa Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya koma gida bayan jinyar da ya yi a London.

Sarkin dai ya yi jinyar ne bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin sa ranar 19 ga watan janairu, inda aka kashe wasu daga cikin 'yan tawaggar sa.

Tun bayan hari ne dai, gwamnatin Kanon ta haramta goyan biyu akan babur domin inganta tsaron jahar.

Dubban jama'a ne dai su ka yi dafifi a kofar fadar sarkin su na murnar dawowar sa.

Karin bayani