Neman taimako a yakin kasar Mali

Shugaba Idriss Deby na Chadi ya bukaci kasashen yammacin Afrika da su hanzarta tura dakaru zuwa arewacin Mali.

Da yake magana wajen bude taron kolin kungiyar yankin yammacin Afrika ta ECOWAS a Yamosssoukro babban birnin Ivory Coast, Shugaba Deby, ya ce, lokacin surutu ya kare, illa na daukar mataki.

Kasar Chadi dai ta tura dakaru fiye da dubu 2 zuwa arewacin Mali domin taimakawa dakarun Faransa da na Mali fatattakar masu tsatstsauran kishin Islama da kuma Azibinawa masu tayar da kayar baya.

To amma kasashen yammacin Afrika na sanyi sanyi wajen cika alkawarin aikewa da dakaru kusan dubu 8 a can.Sojojin Chadi fiye da 20 ne dai aka kashe kawo yanzu.