Amurka za ta ba 'yan tawayen Syria $ 60m

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry
Image caption John Kerry, wanda y gaji Hillary Clinton na rangadin yankin Gabas ta Tsakiya

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya sanar da karin taimako ga 'yan tawayen Syria, a yunkurinsu na hambarar da Bashar Al-Assad.

Mr. Kerry ya ce Amurka zata bayar da kayan agaji da suka hada da magunguna da kayan abinci, kai tsaye ga dakarun 'yan tawayen na Syria.

Haka kuma ya yi alkawarin cewa Amurkar zata samar da dala miliyan 60 ga 'yan tawayen, domin aiwatar da harkokin gwamnati a guraren dake karkashin ikonsu.

Mista Kerry ya bayyana hakan ne a wani taron da aka yi na kawayen Syria a birnin Roma.

Matakin na gwamnatin Amurka, a cewar Mr. Kerry wani karin matsin lamba ne ga Al-Assad ya sauka daga mulki, kuma a kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kimanin mutane 70,000 ne suka mutu, tun fara yakin na Syria a shekarar 2011.

Karin bayani