Za a binciki kisan dan-tasi a Afrika ta Kudu

dan tasin da aka kashe a Afrika ta Kudu
Image caption dan tasin da aka kashe a Afrika ta Kudu

Hukumar dake sa ido kan 'yan sanda a Afurka ta Kudu na gudanar da bincike kan mutuwar wani direban Tasi dan kasar Mozambique, wanda aka sa wa ankwa a hannunsa aka daure a bayan motar 'yan sandan aka dinga jansa a kasa a kan tituna birnin Johannesburg.

Wani hoton bidiyo da wani da ke gefen titi ya dauka, an watsa shi a kafofin labaran kasar.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bayyana hakan a matsayin lamari na baya-bayan nan, na zilla mai tada hankali daga 'yan sandan Afrika ta Kudu.

Kwamishinar 'yan sanda Riah Phiyega ta bayyana matukar damuwa kan lamarin.

Da ma tuni 'yan sanda a Afrika ta Kudun ke fuskantar suka kan kisan mutane 34 wadanda ke yajin aiki a wani wurin aikin hakar ma'adinai bara.

Karin bayani