Thailand da Kungiyar Musulmi sun amince da wata yarjejeniya

Kasar Thailand
Image caption Kasar Thailand

Gwamnatin Thailand da kungiyar musulmi masu gwagwarmaya sun amince da wata yarjejeniya tattaunawa domin kawo karshen rikicin a kudancin kasar.

Tun shekaru tara suka shude ne 'yan gwagwarmayar suka fara tada kayar baya, lamarin da ya kai ga sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da dubu biyar.

Wannan shi ne karon farko da hukumomin Thailand din suka amince da 'yan tawayen,kuma Firaministocin Thailand da Malaysia suka fito fili suka amince da yarjejeniyar.

Dukkannin Kokarin da akayi na kawo karshen fadan ya ci tura.

Wakilin BBC a kudu maso gabashin Asiya ya ce wadanda suke wakiltar 'yan tawayen a wajen tattaunawar daga bangaren dattawan kungiyar, su ne wadanda ke zaune a Malaysia,kuma ba a san wanne irin tasiri suke da shi ba akan galibin matasan kungiyar da suke yaki a Thailand.