Tarihin shugaba Hugo Chavez na Venezuela

Hugo Chavez
Image caption Hugo Chavez ya dade yana zuwa Cuba domin jinyar cutar daji

Hugo Chavez, wanda aka sake zaba domin shafe shekaru shida a matsayin shugaban Venezuela a watan Oktoban 2012, yana cikin shugabannin da suka fi yin fice da jawo cece-kuce a yankin Latin Amurka.

Tsohon sojin ya fara yin suna ne lokacin da ya jagoranci wani juyin mulki da baiyi nasara ba a shekara ta 1992.

Shekaru shida bayan haka, ya sauya akalar siyasar kasar, inda ya lashe zaben shugaban kasa ta hanyar adawa da manyan 'yan siyasar kasar.

Tun daga nan kuma, Mr Chavez ya lashe zabuka da dama da kuri'un jin ra'ayin jama'a, ciki harda sauya tsarin mulki domin baiwa shugaban kasa damar tsayawa takara har iya ransa.

Shugaba Chavez ya ce yana bukatar karin lokaci domin tabbatar da cewa juyin-juya halin 'yan burguzu na Venezuela ya samu gindin zama.

Magoya bayansa sun ce yana magana ne da muryar talakawa; masu adawa da shi sun ce ya zama mai mulkin kama-karya.

A watan Mayun 2012, Mr Chavez ya ce ya warke daga wani nau'i na cutar daji da ba a bayyana ba, bayan da aka yi masa tiyata a shekara ta 2011 da kuma watan Fabrerun 2012.

Sai dai a ranar 8 ga watan Disamban 2012, shugaba Chavez ya ce yana bukatar karin tiyata sannan ya bayyana mataimakinsa Nicolas Maduro, a matsayin wanda zai gaje shi idan bukatar hakan ta kama.

A watan Fabrerun 1992, Mr Chavez ya jagoranci wani yunkuri na kifar da gwamnatin shugaba Carlos Andres Perez da bai samu nasara ba a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan matakan tsuke bakin aljihu.

An shiya juyin mulkin ne bayan da Chavez da wasu jami'an soji suka kafa wata kungiya a asirce da sunan jagoran neman 'yan cin kai na Kudancin Amurka Simon Bolivar.

Mr Chavez ya shafe shekaru biyu a gidan yari kafin ayi masa afuwa. Daga nan sai ya sake kafa jam'iyya sannan ya shiga harkokin siyasa.

A lokacin da Chavez ya hau kan mulki a 1998, tsaffin jini a fagen siyasar kasar sun fara raba-gari da juna.

Sabanin mafiya yawan makwaftanta, kasar Venezuela na bin tafarkin demokuradiyya ba tare da tsaiko ba tun 1958.

Sai dai an zargi jam'iyyu biyun da suka dade a kan mulki da cin hanci da rashawa da almubazzaranci da albarkatun man fetur din kasar.

Dangantakarsa da Amurka ta kara tsami lokacin da ya zargi gwamnatin shugaba Bush da "yakar ta'addanci da ta'adda" lokacin yakin kasar Afghanistan.

Ya kuma zargi Amurka da hannu a juyin mulkin da aka yi masa wanda ya raba shi da mulki na wasu 'yan kwanaki a shekara ta 2002.

Ya farfado sannan ya samu nasara a kuri'ar raba-gardamar da aka kada kan mulkinsa. Daga nan kuma ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2006.

Mr Chavez ya kaddamar da "shirye-shiryen" tallafawa jama'a da dama da suka hada da ilimi da kuma lafiya ga kowa-da-kowa. Sai dai har yanzu akwai talauci da rashin ayyukan yi, duk da arzikin man da kasar ke da shi.

Shugaba Chavez ya kware sosai wurin magana, wanda ya ke nuna wa a shirin talabijin din da ya ke yi duk mako (Hello President), inda yake magana kan manufar siyasarsa, da tattaunawa da baki da rera waka da kuma rawa.