Ranar alhamis za a bude bankunan kasar Cyprus

Masu dibar kudi a wani bankin Cyprus
Image caption Masu dibar kudi a wani bankin Cyprus

Gwamnan babban bankin Kasar Cyprus, Panicos Dimitriades, ya dauki alkawarin yin kokarin sake bude bankunan Kasar a ranar Alhamis.

Bankunan dai sun shafe kusan makonni biyu ke nan yanzu suna rufe domin hana mutane kwashe kudadensu na ajiya, a yayinda ake tattaunawa a kan shirin ceto tsarin bankunan Kasar daga durkushewa.

Mr Dimitriades, ya tabbatar da cewa za'a sanya harajin kusan kashi arba'in cikin dari a kan masu ajiya a banki wadanda kudadensu suka haura dala dubu dari da talatin, kuma ya yi gargadin za a takaita wasu abubuwa.

Wani daftari da BBC ta gani ya nemi a sa- ido kan harkokin kudi da suka hada da takaita yawan kudin da mutum zai iya cira daga banki, da kuma takaita iya kudaden da za 'a iya fitarwa daga kasar zuwa kasashen ketare.

Bankin 'yan kasuwa a kasar mafi girma dai ya yi watsi ta murabus din shugaban bankin.

Ya dai gabatar da murabus din nasa ne bayan da gwamnati ta nada wani mai gudanar da harkokin bankin na musamman.

Karin bayani