Unicef ta yi gargadi kan makomar yara a Syria

Tambarin hukumar kula da yara ta Unicef
Image caption Tambarin hukumar kula da yara ta Unicef

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadi kan makomar yara da dama a kasar Syria.

A wani rahoto da aka fitar domin dacewa da zagayowar shekaru biyu da fara rikicin kasar ta Syria, hukumar kula da yara ta Majalisar, Unicef, ta ce miliyoyin yara a Syria na tasowa ba tare da sun san komai ba sai tashin hankali.

Wakiliyar BBC ta ce hukumar ta Unicef, ta ce a cikin mutane miliyan hudu da ke bukatar agaji a Syria, miliyan biyu 'yan kasa da shekaru 18 ne, yayin da fiye da rabin miliyan ke kasa da shekaru biyar.

Unicef ta kara da cewa rashin kudi na kawo cikas a yunkurinta na sama musu ingantaccen ruwan sha da allurorin rigakafi.