Kotun kolin Amurka na sauraren karar auren jinsi daya

Zanga zangar fafutikar halatta auren jinsi daya
Image caption Zanga zangar fafutikar halatta auren jinsi daya

Kotun Kolin Amurka ta fara saurarar daya daga cikin kararraki biyu da aka kai gaban ta, da masu fafutikar goyan bayan auren jinsi guda suka shigar gabanta.

Lauyoyinsu suna kwatanta hana auren jinsi guda a California, da aure tsakanin wadanda launin fatarsu ta banbanta, wacce kotu ta sauyawa hukunci a shekarun 1960.

Amma daya daga cikin alkalan Kotun ya bayyana dari dari game da shari'ar, ya na mai tambayar ko mai yasa ma har sai an kai batun gaban kotu ma gaba daya.

Ba a sa ran yanke hukunci a watanni da dama masu zuwa, amma wakilin BBC a Washigton ya ce ga alama kotun tana kaucewa yanke wani hukunci ne na musamman ta kowanne bangare.