APC ta 'tallafawa' jama'ar Borno da Yobe

APC ta 'tallafawa' jama'ar Borno da Yobe
Image caption Jama'a da dama ne dai suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a jihohin biyu

Gwamnonin gamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya da ke kokarin kafa jam'iyyar APC, 'sun bayar da gudummawar naira miliyan 200' ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin Borno da Yobe.

"Domin nuna alhini ga gwamnatoci da mutanen Borno da Yobe, mun zo domin ganewa idanunmu halin da ake ciki, kuma muna farin cikin ganin yadda al'amura suka inganta musamman a Maiduguri," a cewar sanarwar da gwamnonin suka fitar.

Sai dai an samu tashin wasu bama-bamai a unguwani biyu na birnin na Maiduguri, a daidai lokacin da gwamnonin ke taron, a ci gaba da kokarinsu na kafa babbar jam'iyar adawa ta All Progressive Congress domin kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki.

Gwamnonin jihohin Borno, Edo, Ekiti, Imo, Lagos, Nasarawa, Ogun, Osun, da Yobe ne suka samu halartar taron, yayin da gwamnonin Zamfara da Oyo suka bayar da uzurin rashin halarta.

Hare-hare

"Sabanin yanayin tashin hankali da ake bayyanawa a jihohin biyu, munga jama'a suna fita domin yin harkokinsu na yau da kullum ba tare da wani fargaba ko tashin hankali ba", aecwar sanarwar.

Harin bam din na ranar Alhamis ya faru ne a unguwannin kwastan na Bolori, inda ya hallaka sojoji biyu da kuma fararan hula da dama.

Har yanzu dai ba wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin tada bama-baman.

Sai dai jihar ta Borno ta sha fama da hare-haren kungiyar Jama'atu Ahlissunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram.

Karin bayani