Gargadi ga masu satar fasaha a Internet

Click
Image caption Amurka ta bi sahun Faransa da New Zealand wajen kaddamar da tsarin

An fara amfani da wani sabon tsari dake aike wa da gargadi, sannan a hukunta wadanda ke satar fasaha tare da rarraba fina-finai da wakoki da wasannin kwamfuta ta haramtacciyar hanya ta intanet a Amurka.

Sabon tsarin da ake cewa "Six Strikes" a Turance na da goyon bayan manyan kamfanonin da ke samar da intanet a kasar.

A karkashinsa wadanda ake zargi da maimaita keta hakkin mallaka za a tura musu sakon gargadi sau shida daga nan kuma za a takaita musu amfani da intanet, amma ba za a hana su kwata-kwata ba.

Masu fafutuka da ke adawa da tsarin sunce an baiwa kamfanonin wuka da nama, saboda haka sun fi son a baiwa wata hukuma mai zaman kanta nauyin kula da tsarin.

Amurka ta bi sahun Faransa da New Zealand wajen kaddamar da tsarin.

Kasashen da ke ikirarin cewa tsarin ya rage satar fasaha da kusan rabi.

Karin bayani