'Jonathan zai iya tsayawa takara a 2015'

Goodluck Jonathan
Image caption Tuni dai fastocin shugaban na neman takara a 2015 suka fara yawo a kasar

Wata kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta ce shugaban kasar Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takara a zaben shekara ta 2015.

Kotun ta ce sai a shekara ta 2015 ne zai kammala wa'adinsa na farko.

Goodluck Jonathan ya fara wa'adinsa ne bayan zaben da aka yi masa a shekara ta 2011.

Ta kara da cewa mulkin da ya hau a shekara ta 2010 bayan rasuwar marigayi Shugaba Umaru 'Yar'adua, ya zama wajibi ne domin cike gibin da aka samu kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

Wani dan jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ne Cyriacus Njoku, ya shigar da karar yana neman kotu ta hana shugaban tsayawa takara bisa hasashen cewa ya yi wa'adi biyu a kan karagar mulki.

'Dauki ga 'yan Najeriya'

Wakiliyar BBC da ta halarci zaman kotun Raliya Zubairu, ta ce lauyoyin da suka wakilci jam'iyyar PDP sun nuna farin cikinsu ga wannan hukunci, sai dai wanda ya shigar da karar ya ce zai daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

"...hukuncin nasara ce ga tsarin demokuradiyyar Najeriya...kuma ya kawo karshen takaddamar da ake yi kan ko shugaba Jonathan na da izinin tsayawa takara a 2015 ko kuma a'a," a cewar wata sanarwa da jam'iyyar PDOP ta fitar.

Mai magana da yawun jam'iyyar Olisa Metuh ya ce yanzu ya rage ga 'yan Najeriya da kuma jam'iyyar su yanke hukunci ta hanyar da ta dace idan shugaban ya nuna sha'awarsa.

Sanarwar ta kara da cewa hukuncin kotun ya kare kasar daga 'yan barandan siyasa da ke kokarin dora kawunansu ta karfi da yaji kan 'yan Najeriya.

"Amma a yanzu bangaren shari'a ya kawowa 'yan Najeriya dauki ta hanyar wannan hukunci".

Masu lura da al'amura na ganin wannan gwagwarmayar neman takara a 2015 da aka fara tun yanzu, na iya kawo tsaiko ga alkawuran da 'yan siyasa suka dauka na inganta rayuwar mutane ganin cewa basu dade da hawa mulki ba.

Karin bayani