Mutane talatin sun hallaka a Bangladesh

Rikici a kasar Bangladesh
Image caption Rikici a kasar Bangladesh

Akalla mutane talatin ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu daruruwa kuma suka jikkata a zanga-zangar da ake a fadin kasar Bangladesh.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan yankewa wani jagoran wata kungiyar musulmi hukuncin kisa, kan rawar da ya taka lokacin yakin neman 'yancin kasar daga Pakistan, shekaru sama da arba'in da suka wuce.

Wata kotu ce ta musamman ta samu Delwar Hussain Sayyadi na jam'iyyar jama'atu islami da laifin kisan kai da fyade da kuma azabtarwa.

A rikicin baya-bayan nan da akayi, an kashe jami'an 'yan sanda uku a gundumar arewacin Gaibanda lokacin da magoya bayan malamin su ke tarzoma.