Dubban mutane sun tsere daga Congo

Sojoji a Congo
Image caption Rikici tsakanin 'yan tawaye a Congo

Dubban jama'a sun tsere daga jamhuriyar dimokradiyyar Congo zuwa cikin Uganda mai makobtaka bayan mummunan fada tsakanin bangarori biyu da basa ga maciji da juna a kungiyar 'yan tawaye ta M23.

Fadan ya barke ne a gundumar Rutshuru arewa da gabashin birnin Goma.

A jiya Alhamis kungiyar M23 ta ce ta kori shugabanta Jean Marie Runiga inda ta zarge shi da cin amana.

A ranar lahadin da ta gabata ma dai an kashe mutake akalla goma a arangama tsakanin magoyan Runiga kuma jagoran sojin 'yan tawayen.

Karin bayani