'Yan Democrats da Republican a Amurka na zargin junan su

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

'Yan jam'iyyar Democrats dana Republican a Amurka na zargin junan su kan gaza daukar matakin kaucewa zabtare kudaden da gwamnati ke kashewa.

Kudaden dai sun tasamma dala miliyan dubu tamanin da biyar,wanda zai fara aiki ranar juma'a.

Asusun bada lamuni na duniya wato IMF, ya yi gargadin cewa wannan zabtare kudi zai shafi bunkasar tattalin arziki na duniya.

Shugaba Obama zai gana da shugabannin majalisar dokokin Amurkan, domin cimma matsaya akan batun.

Wakilan kafafan yada labarai sun ce, za a aiwatar da matakin zabtare wadannan makudan kudade da gwamnati ke kashewa ne daki-daki cikin watanni masu zuwa.