Sojan Amurka ya amince da laifin bayyana sirrin gwamnati

Bradely Manning na sauka daga motar jami'an tsaro
Image caption Bradely Manning na sauka daga motar jami'an tsaro

Sojan Amurkar nan Bradely Manning ya amince cewa ya mika dimbin bayanan sirrin gwamnati ga shafin yanar gizon nan mai kwarmata bayanai na Wikileaks.

Amma kuma, Bradely Manning wanda ya yi aiki a Iraqi,ya ki amincewa da tuhumar da ake masa.

Yanzu dai an tabbatar da dalilan da suka sa Bradely Manning ya dauki wannan mataki na kwarmata bayanan sirri mafi girma da aka taba samu a tarihin Amurka.

Ya shaidawa Kotun sojin cewa ya aikata hakan ne bayan kaduwar da yayi kan abinda ya kira yadda Amurka ke cafkewa tare da hallaka abokan gabatar ta, a wani faifan bidiyo dake nuna wani harin jirgin helicopter a Iraqi.

Mr Bradely Manning dai ya ce, ya so ya ingiza wata zazzafar muhawara ne kan yadda Amurka ke sa hannunta cikin yakin dake faruwa a kasashen Iraqi da Afganistan.

Alkalin koton ya amince da amsa laifuka goma cikin ashirin da biyun da wanda ake tuhumar yayi, sai dai Mr Bradely Manning ya musanta babbar tuhumar da ake masa na taimakawa abokan gabar Amurka.