Mutane 11 sun rasu bayan Tirela ta fadi a Koko

Hatsarin mota a Najeriya
Image caption Tirela ta fadi a Birnin Kokon jahar Kebbi

A Najeriya rahotanni daga garin Koko na jihar Kebbi da ke arewacin kasar na cewa mutane goma sha daya ne suka mutu, wasu mutanen ashirin da hudu kuma sun samu raunuka, sakamakon faduwar wata Tirela mai daukar kaya da sanyin safiyar ranar asabar.

Tirelar dai ta fito ne daga birnin Lagos zuwa garin Jega, kuma ta na makare ne da buhuna da mutane.

Wani wanda ya shaida lamarin yace dukkanin wadanda su ka rasun matasa ne majiya karfi wadanda su ka fito daga jahohin Kebbi da kuma Sakkwato

An kuma garzaya da wadanda su ka jikkata zuwa babban asibitin garin Koko inda suke karbar magani.

Ana dai yawan danganta hatsarin mota da ake yawan samu a Najeriya da rashin tituna masu kyau, da ganganci daga bangaren direbobi da kuma rashin bin ka'idar tuki.

Karin bayani