Amurka za ta rage kashe kudade

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya rattaba hannu kan dokar aiwatar da batun zaftare yawan kudaden da gwamnati ke kashewa.

Kudaden dai sun tasamma dala biliyan tamanin da biyar.

Dukkannin 'yayan jam'iyar Democrats da na Republicans sun nuna adawa da batun rage kudaden, sai dai bangarorin biyu sun gazan cimma yarjejeniya kan yadda zasu kawar da batun.

A shekaru biyun da suka gabata ne dai aka bullo da wannan yunkuri, aka kuma tsara shi ta yadda zai zaburar da 'yan siyasar Amurka wajen daidaita al'amuran da suka shafi harkokin kashe kudade.

Kusan rabin zaftare kudaden zai fito ne daga kasafin kudin bangaren harkokin tsaron kasar.

Shugaba Obama na gargadin cewa zaftare kudaden zai shafi yanayin samar da ayyuka dama habbakar tattalin arziki.