Dakaru a Afganistan sun nemi gafara kan kisan wasu yara

Dakarun kasar Australia
Image caption Dakarun kasar Australia

Dakarun kasa da kasa a Afganistan ISAF, sun nemi gafara game da kisan wasu yara makiyaya 'yan kasa da shekaru bakwai a lardin Uruzgan.

Yaran sun hallaka ne bayan da wani jirgi mai saukar angulu na dakarun kungiyar tsaro ta NATO ya bude musu wuta.

Wata sanarwa daga dakarun sojin ta ce sun aikata kisan ne bisa kuskure, bayan da suka zaci cewa 'yan kungiyar Taliban masu tada kayar baya ne, kuma sun ce za a biya iyalansu diyya.

Gwamnan lardin Uruzgan ya ce sojojin Australiar sun hallala yaran ne a bisa kuskure.

Jami'an kungiyar tsaro da NATO da na kasar Australia sun bayyana wannan kisa da cewa abin takaici ne.

A wata sanarwa, mai magana da yawun dakarun kasa da kasa na Afganistan, Janar Gunter Katz ya nemi gafara game da kisan.

A watan da ya gabata ne hare-haren dakarun kungiyar tsaro ta NATO ya hallaka fararen hula goma a lardin Kunar, da ya sa shugaban Afganistan Hamid Kharzai ya dakatar dakarun kasa da kasa kai hari da sama a yankunan gidajen jama'a.