An kashe akalla mutane 15 a Bangladesh

Zanga-zanga a kasar Bangladesh
Image caption Zanga-zanga a kasar Bangladesh

An kashe akalla mutane goma sha biyar a Bangladesh yayin da tashin hankali ke karuwa tsakanin 'yan sanda da magoya bayan wani jagoran jam'iyyar musulunci da aka yankewa hukuncin kisa ranar Alhamis saboda aikata laifukan yaki.

Tun daga farkon yajin aiki na kwanaki biyu magoya bayan jam'iyyar ta Jamaat-e-Islami sun bazama cikin kasar, su na farwa ofisoshin 'yan sanda, da tashohin jiragen kasa da kuma gine-ginen gwamnati

Wakilin BBC yace tun daga lokacin da aka soma tashin hankalin an kashe mutane fiye da hamsin.

Karin bayani