An zargi mutum 2 da yunkurin juyin mulki a Benin

Shugaba Yayi Boni na Benin
Image caption An yi zargin kifar da gwamnatin Yayi Boni

Hukumomi a jamhuriyar Benin sun ce, sun kama wasu mutane biyu da suke zargi da kokarin yiwa gwamnatin shugaba Yayi Boni juyin mulki.

A wata sanarwa, babban mai gabatar da kara na kasar, Justin Gbenameto yace, wani soja mai mukamin kanar da wani dan kasuwa sun shirya kafa gwamnatin soja a jamhuriyar Benin bayan sun hana shugaba Yayi Boni komawa kasar yayin da yake ziyara a kasashen waje.

Babban mai gabatar da karan yace, ana tsare da mutanen biyu ne fiye da mako guda da ya gabata.

Shugaba Yayi Boni wanda yake kan mulki tun shekarar 2006, ya tsallaka kokarin kashe da aka yi da kuma wani kokari na sa guba a abincinsa