Chadi ta ce sojojinta sun kashe wani jagoran 'yan tawaye a Mali

Sojojin kasar Chadi
Image caption Sojojin kasar Chadi

Kasar Chadi ta ce sojojinta sun kashe daya daga cikin kusoshin 'yan kungiyar mayaka masu kaifin kishin Islama a yankin arewacin Afirka.

Ana dai zargin Jagoran kungiyar mai suna Mokhtar Belmokhtar da aka fi sani da '' Ido daya'' , da bayar da umarnin kai wani hari a masana'antar Iskar gas ta kasar Algeria a cikin watan Janairu.

Mutane fiye da talatin din da aka yi garkuwa da su ne suka hallaka harin.

Sojojin na kasar Chadi dake cikin tawagar dakarun kasashen Afirka ta yammar da aka tura kasar Mali, domin fatattakar 'yan tawaye masu kishin Islamar sun ce sun kashe Mokhtar Belmokhtar a wani hari da suka kai sansanin 'yan tawayen.

Mukaddashin hafsan sojin kasar ta Chadi, Janar Zakaria Ngonbongue ne ya sanar da batun kisan na Belmoktar, inda ya ce sun yi kaca kaca da babban sansanin 'yan tawayen.

Bayanan daga sojojin na kasar Chadin na zuwa ne kwana guda bayan da suka yi ikirarin cewa sun hallaka kwamanda kungiyar Al-Qaeda, Abu Zeid.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da mutuwar dukkannnin mutanen biyu.

Idan dai ta tabbata cewa an kashe Mokhtar Belmoktar, zai zama wani babban rashi nega kungiyar mayaka 'yan tawayen dake yankin arewacin Malin.

Sai dai ba wai zai nuna cewa an kawo kasrhen yakin ba, wanda 'yan tawayen ke ci gaba da nuna turjiya.

Belmokhat dai yayi ikirarin cewa shi ya jagoranci kai hari kan masana'antar sarrafa Iskar gas dake gabashin kasar Algeria a farkon wannan shekarar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da talatin, ciki har da wasu ma'aikata 'yan kasshen waje.