An kwantar da Sarauniya Elizabeth a asibiti

Image caption Sarauniya Elizabeth da 'yar ta Anne

An kwantar da Sarauniyar Ingila Elizabeth a wani asibitin birnin London sakamakon fama da take da ciwon ciki dake haddasa amai da gudawa, da kuma ƙullewar ciki.

Ta dai soma rashin lafiyar ne tun daga karshen makon da ya gabata, kuma hakan tasa an soke ziyarar da aka shirya zata kai zuwa yankin Wales ranar jiya Asabar.

Wakilin BBC yace, ɗan lokacin da sarauniyar zata kwashe asibiti, karon farko cikin shekaru goma, zai bata damar samun hutu, kuma zai masu yi mata hidima damar nazari akan yawan ayukan da take yi.