Cardinals na cocin Roman Katolika suna taro

Image caption Manyan limaman cocin Roman Katolika masu matsayin Cardinal

Manyan malaman ɗarikar roman katolika daga sassa daban daban na duniya sun fara tattaunawa a asirce a birnin Roma gabanin zaɓen wanda zai gaji Paparoma Benedict.

Kakakin fadar Vatikan din Fada Thomas Rosica ya ce kawo yanzu tattaunawar na tafiya yadda ya kamata kuma tana nuna irin yadda aka damu da cocin a duk fadin duniya.

A lokacin tattaunawar za su yanke shawara kan ranar da za a gudanar da zaben sabon paparoman.

Yayin da limaman cocin suka shiga fadar Vatikan din, wadanda ke kula da su sun tabbatar ba kowa a tare da su dama masu kamarorin daukar hoto.

Masu aiko da rahotanni sun ce an ɗauki tsauraran matakan hana fitar da bayanan abinda ke gudana yayin zaben.

Masana masana harkokin sadarwa za su toshe duk wata kafa ta sadarwa a dakunan kwanan malam cocin, sannan ba za su yi amfani da wayoyin salularsu ba a yayin zaɓen.