Cardinals za su fara taron zaben Fafaroma

Masu mukamin Cardinals a cocin Roman Katolika a yau Litinin za su fara wannan taron sirrin wanda za'a kwashe mako daya ana yi domin zabar sabon Fafaroma bayan murabus din din da Fafaroma Benedict ya yi a ranar alhamis din da ta gabata.

Wanda su ka zaban ne zai jagoranci cocin katolika mai sama da mabiya biliyan daya a duniya.

A mako mai zuma ne ake sa ran za'a fara zaben sabon fafaroma, amma ya zuwa yanzu dai ba a sanya ranar kada kuri'ar ba.

Masu mukamin Cardinals daga fadin duniya dai na ci gaba da isa birnin Rome domin zaben sabon Fafaroma da zai jagoranci cocin Roman Katolika a fadin duniya.

Kashi biyu cikin uku na Cardinals din da ake da su a duniya sun riga sun isa birnin na Rome a karshen makon da ya gabata.

Kasar Burtaniya dai ba za ta samu wakilci ba ba saboda murabus din da Cardinal Keith O'Brien ya yi, bayan ya amince da zargin yin lallata da ake masa.

Archbishop din Westminster da ya yi murabus wato Cardinal Cormac Murphy O'Connor, zai halarci taron share fage, amma bashi da damar yi zabe saboda ya haura shekaru tamanin.

Amma dai yayi zabe a lokacin da aka zabi Pope Benedict a shekara ta 2005.

A yanzu haka dai za'a tsaurara matakai a Vatican musamman ma game da samun bayanai har sai an zabi sabo fafaroma.